29 Maris 2026 - 14:18
Source: ABNA24
Jaulani Ya Tura Dakaru Da Makamai Zuwa Kan Iyakar Iraqi Da Siriya 

Akwai yiwuwar ɓarkewar yaki da sabuwar Syria da Isra'ila nan ba jimawa ba bayan barazanar da Isra'ila ke yi na a kashe shugaban Siriya idan har Jaulani yaki zartar da qudirin Amurka da Isra'ila 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Binguir", ministan tsaron cikin gida na gwamnatin Sahayoniya mai tsattsauran ra'ayi ya kira da cewa: Al-Julani kamar kan maci ne kuma ya kamata a shirya kai masa hari da zai kashe. Yakin da ake yi da sabuwar Syria ya kusa.

Isra'ila tana ganin Jaulani yayi ƙasa a gwiwa wajen taimaka mata a yaƙin da ya ke yi Iran da Hizbullah don haka take kira da kawar da shi tana me ganin yana mata ungulu da kan zabo. A gefe guda kuma Jaulani ya aike da manyan kayan soji zuwa kan iyakar Iraki. Gwamnatin Abu Muhammad Jaulani, shugaban 'yan tawayen Syria, ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, ya aike da sabbin kayan aiki da dakaru zuwa kan iyakar Syria da Iraki. "Ƙarin dakarun agaji sun isa kan iyakar Syria da Iraki a safiyar yau kuma an jibge su a kewayen yankin Al-Hari da ke kan iyakar," in ji wata majiyar soji a ma'aikatar tsaron Al-Jaulani. Ya ce kayan aikin sun hada da sojoji da dama da motocin soji da manyan makamai, kuma ya yi ikirarin cewa manufar matakin shi ne "hana duk wani kutsen tsaro a kan iyakar Syria da Iraki." Majiyar ta kuma ce kayan aikin da aka aika a yau su ne kaya karo na uku da aka tura zuwa yankunan kan iyaka tun bayan fara yakin Amurka da Isra'ila da Iran. Masana sun jaddada cewa Al-Jaulani ya aike da dakarun ne don aiwatar da umarnin Amurka da Isra'ila domin matsa wa dakarun Iraqi lamba, musamman dakarun Hashdush Sha'abi. 

Majiyar da ke da alaka da Al-Jaulani ta bayyana cewa, "Dakarun gwamnati sun kama wasu Mutane na shahdush Shabi da Iran a cikin yankin Syria, wadanda dukkansu sun shiga cikin sirri ta kan iyakar Syria da Iraki." Bugu da kari, wata majiya da ke da alaka da Al-Jaulani ta ce "ya damu matuka" sakamakon hare-haren da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami suka kai kan sansanonin Amurka a Syria. Majiyar ta yi ikirarin cewa, hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan sansanonin Amurka da ke lardin Al-Hasakah da Deir Ez-Zor da ke Syria, sojojin Iraki ne suka kai su.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha